ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 5 by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 5 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN  BOOK 2  CHAPTER 5   by Sumayyah Abdul-kadir Cikin dan lokacin nan mun tattauna abubuwa da dama mun kara fahimtar juna. Har zuwa lokacin na kasa tambayar shi sunan shi. Sai wurin karfe goma Haulatu ta fargar damu, da kyar muka katse hirar muka fito zuwa mota.  Ina ganin Ummi da Haulatu na gulma suna rada da dariyar shegantaka ko kula su ban yi ba. Don na san da ni suke. A kan hanya ma hirar muke yi. Ya gaya min ya yi dukkan karatunshi ne a Taiwan inda ya karanta harshen Larabci ziryan. Shi da Abdullahi ‘ya’ yan family friends ne, haifaffun garin Dambatta.  Da kyar muka iya yin sallama don sai da Ummi ta shige ta barmu. Sai shigowar hancin motar Yaya Mufty ne yasa muka yi sallama ya jira fitowar shi da yin parking din shi suka yi hannu, sannan ya shiga motarsa ya tafi. Har zai fita get ya dawo ya yi min horn na juyo “Phone no na manta Fa’izah”’.  “Ni da Ummi bamu da waya”.  “Saboda me?”  “An hana mu rikewa ne”.  Hannu yasa ya dauko tashi a gefe, “Ki rike wannan saboda ni Fa’izah.…