ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 2 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 2 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 2 by Sumayyah Abdul-kadir Malam Hassan. Ina jama’ar gidan suka tafi ne? Mantawa aka yi yau muke graduating? Babu wanda ya je mana daga Giwa, Zaria har nan cikin Kaduna?” Ya ce, “Hala mantawa kuka yi yau ake daurin auren Zanirah da Alh. Aliyu???” Wallahi baya ga wannan ban sake jin komai ba, ban sake sanin inda kaina yake ba. Sai tsintar kaina na yi a asibitin Jinya dake cikin garin Kaduna, Ummi na gefen kaina tana mini firfita. Na soma kokarin tuno abin da na ji (DAURIN AUREN ZANIRA DA ALTYU). Na fashe da wani gursheken kuka a cinyar Ummi, ita ma Ummi kuka take, na tabbata kukan tausaya mana ne ni da Yaya Aliyu, cewa take “Ya aka yi haka Fa’izah? Garin ya ya ni ban san zancen ba? Ya ya aka yi haka? Na dauka ke za a baiwa Yaya Aliyu?” Na mike zumbur ina layi na ce, “Ummi ya zama dole in je Giwa a yanzun nan, dole ne in je Giwa kada Zanira ta dauka ina bakin cikin auren ta da Yaya Aliyu ne, ta wuce haka a gareni, tashi mu tafi Ummi”. Ummi ta share hawaye t…