ZABIN RAI CHAPTER 1

ZABIN RAI CHAPTER 1
ZABIN RAI CHAPTER 1 This book is  free from beginning to end.2 ***    ***     *** A hankali ya bude idonsa sai kuma ya maida idon ya rufe har sai da wayar ta sake ringing. Wannan karon yayi saurin bude idon ya sauka daga kan gadon yana kallon kyakkyawar mace dake gefensa tana bachi, hannu ya kai kamar zai shafa fuskarta sai kuma ya fasa sakamakon wayarsa da tai ringing. Kallon kwayar yai kamin yabkai hannu ya dauka.+ “Sadam kai kadai muke jira fa” “On my way Dad” Ya fada yana shafa sumar kansa, sannan ya aje wayar yana hamma, da alama bachin be isashe ba a haka ya tashi ya nufi bathroom, a gaggauce yai wanka ya fito sanye da bathrobe ya nufi gaban madubi. Cikin kankan lokaci ya shirya ya feshe jikinsa da expensive perfume, wani bangare ya nufa na bedroom, hannu ya kai ya danna wani dan karamin maballi dake gefensa gurin sai ga wata katuwar kofa mai cushion ta rabu biyu, ciki ya shiga ya sai gashi cikin wani dan madaidacin dakin mai dauke da kayan ado na zama kama daga kan tufafi, agogo, ta…