YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 2 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 2 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 2 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng Jiya mun tsaya inda Mamaki ya sake rufe shi, “Da ma na san wadannan ‘yan matan aljanu ne.” Kwanciyarsa ke da wuya sai barci mai Karfin gaske ya dauke shi har sai da dokinsa ya zo ya yi haniniya sau biyu. Nan da nan ya farka. Ya tashi ya yi sallah ya roki Allah nasara da kariya, kuma cikin gaggawa ya dauki tulu ya tafi yana debo ruwa ZAMU TASHI zubawa a rijiya har sai da ya zuba tulu goma. Bayan ya kammala, sai ya je wurin dokinsa yana shafa shi, kuma ya fahimci ba don dokin ba, to lallai da ya makara, alhali kuwa Shehi ya gargade shi a kan haka. Gari na wayewa tangaran sai ya zauna a Karkashin wata bishiya yana tunanin abin da ya gani daren jiya, irin wakoKin ‘yan matan nan, ya kuma tsunduma cikin begen kyan yarinyar nan da dadin muryarta da kuma irin kwarjininta, ya dai tabbatar wa kansa cewa lallai wadannan ‘yan matan aljanu ne. Babban abin bakin cikin ma a wurinsa shi ne irin yadda bai sami da…