YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 1 BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 1 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 1 BY HARUNA USMAN SABON LITTAFI DAGA WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG  HAJI Hamidu dan Usman mutum ne da Allah Ya yi wa baiwar ilmi da aiki da shi, ga hankali da hakuri da riKon amana da kuma rashin girman kai. Daidai gwargwado kuma yana cikin rufin asiri.  Babbar dacewa ita ce irin yadda Allah Ya albarkace shi da mace ta Kwarai, wadda samun irin ta sai an tona ta bangaren sanin ya kamata da hakuri da kyau da cikar halitta. Sunanta Ramlah.  Www.bankinhausanovels.com.ng  Ma’‘auratan suna da ‘ya’ya maza da mata, amma manyan da suka isa misali su uku ne. Babban sunansa Idrisu, mai bi masa kuma Abubakar wanda suke kira Habu, sannan sai Yahaya. Dukkan su sun sami ilmi daidai gwargwado. |  Wani abin sha’awa shi ne irin yadda wadannan samari ba su bar komai na kyawawan halaye da siffofin iyayensu ba, hakan ya sa halayyarsu ta zama abar misali kuma kyan halittarsu ya zama abin tsegumi a gari. }  Fara jin dadi da kuma taka wani mataki na ilmi ne  suka sa wadan…