YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 4 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 4 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 4 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng A JIYA MUN TSAYA Sarkin aljanu Sham’una ya ci gaba da zuwa har ranar Juma’a. A ranar Asabar wasu daga cikin Musulmin ‘yan matan nan suna zaune suna karanta wata sura daga cikin AlKur’ani mai girma, sai ga aljana Dailanu. Tana isowa ta ji karatun nan sai hankalinta ya tashi, ta rude jikinta ya yi sanyi, ta ji ba abin da take so kamar karatun, saboda haka sai ta sami wuri ta koma gefe ta zauna har sai da suka gama. Kafin su kammala sai ga aljana tana hawaye saboda irin firgicin da karatun ya jefa mata. Suna gamawa sai suka ga Dailanu ba kamar kullum ba, ZAMU TASHI don hankalinta a tashe ya ke har yadda su ma sai da suka ji tsoro, suna zaton ko wani abu ya faru ne. Yarinya Nur ta tambaye ta, “Ya ke wannan kyakkyawar yarinya, yau mene ne lamarinki muka gan ki cikin wani irin hali da ba mu taba ganin ki a cikin irin sa ba, kuma na bacin rai. Ko kuwa mun bata miki rai ne? To a gaskiya ba da niyyarmu …