YAKANA BOOK 1 KARSHE CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

YAKANA BOOK 1 KARSHE CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
YAKANA BOOK 1 KARSHE CHAPTER 7  BY SUMAYYAH ABDULKADIR Da sauri Inna ta ce,  “Ka ga Fati can tana tare mota, yi kwana mu dauke su”. Ya yi kamar bai ji ba, ya karawa motar shi gudu. Inna ta yi salati ta ce, “Baka ji ni bane? ‘Ya’yan ka fa ta dauko daga makaranta!”. Sai a sannan ya juya, tuni ta tare tasi suna kokarin shiga. Ya ce, “Ai sun shiga mota ma hadu a can”.  Inna ta yi shiru tana mamaki, har suka iso gidan su Fati ba su shigo ba, don ba za ka hada motar gida da ta haya da ke yin tsaye-tsaye ba.  Tun daga soron gidan yake jiyo kukan Baby Nana Khadijah. Ya rintse ido tsigar jikinshi na tashi. Inna ce ta yi sallama ya biyo bayan ta. Yaya suka tarar tana ta fama da Baby Nana, wadda ke ta tsandara kuka kamar ta tsaga gidan ta ki karbar madarar da take bata.  Ta amsa musu sallama cikin sakin fuska da walwala, ta shimfida musu sabuwar tabarma, sannan ta mikawa Inna Baby Nana. Yaya ta dubi Sulaiman ganin yadda ya rame ya yi kasumba, sai ta ji hawaye sun ciko idon ta.  Ta ce,  “Me nake gani hak…