YAKANA BOOK 1 CHAPTER 6 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
YAKANA BOOK 1 CHAPTER 6 BY SUMAYYAH ABDULKADIR Da ya ga wannan ba za ta yi mishi ba, sai ya nufi ofishinsa ya murda kofar ya shiga, ya jingina da kofar ya soma tunanin wasu al’amura da ya lura Hadiza na boye mishi, da yawan waya da take yi da Dr. Bunza na mene ne? Sannan da kwayoyin maganin da ya gani a leda babu suna babu takardar su a karkashin gadon su. Ya yi wani irin huci mai zafi, “Akwai wata matsala wadda da alama dadaddiya ce”. Ya tuno furucin Dr. Abdullahi. A sukwane ya bude kofar ya fita ya nufi ofishin Dr. Bunza a psychiatry. Dr. Bunza na rubuce-rdubuce a file suna hira da Dr. Karaye, Dr. Sulaiman ya bankada kofar ofishin ba tare da ya yi sallama ko neman izinin shigowa ba, ya kai wa Dr. Bunza shaka ya ce, “Gara in kashe ka, kafin ka kashe ni….”. Dr. Karaye ya soma kokarin kwatar Dr. Bunza wanda ya sha_ shaka matuka, duk idanun sun yo waje. Ya ce, “Ba zan cika shi ba, sai ya gaya min abin da ke damun matata, da magungunan mene ne yake dirka mata?” Dr. Bunza ya ce, “Ka yi ha…