YAKANA BOOK 1 CHAPTER 3 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
YAKANA BOOK 1 CHAPTER 3 BY SUMAYYAH ABDULKADIR wannan satin za a rufe”. Ta ce, “Baba bai dawo bane?” Yaya ta ce, “Ya dawo tun yamma, ya tafi dubiyar dan gidan Malam Abdu ne babur ya buge shi dazu”. Ta ce, “Allah ya sauwake, Fati na ciki ko”. Yaya ta ce, “Yanzu ta gama cin abinci ta shige ciki tana rehearsal, jibi za su yi musabakar jiha kuma ita za ta wakilci jihar Kano, kin san Fati ba daga nan ba”. Cikin alfahari da kanwar tata a zuciyarta, Hadiza ta tura kofar dakin cikin sallama, Fati ta diro daga gado ta rungume ‘yar uwarta tana yi mata oyoyo. Hadiza ta dubi Fati sama da kasa, ta zama cikakkiyar budurwa sosai. Ta kama baki “Fati girma haka?” Fati ta yi murmushi, kumatunta duka suka lotsa gwanin sha’awa, wushiryarta ta fito siririya da ita. Hadiza ta ce, “Wane course aka samu?” Ta ce, “Course din da na nema ne (Islamic Studies)”. Ta ce, “Masha Allah, da an je kuma sai a Samo saurayi, irin wannan girma haka Fati?” Ta ji kunya ta boye fuskarta cikin tafukanta, ta ce, “Ai hijabi zan …