YAKANA BOOK 1 CHAPTER 2 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
YAKANA BOOK 1 CHAPTER 2 BY SUMAYYAH ABDULKADIR ba, a kan diya mace. Sai dai shi a ce ana son sa yana hura hanci, kada hakan ya janyo raini, baya fatan hakan ya kasance sakayya ce Allah ya yiwa dimbin matan da ke binsa agindi-agindi don ya so su yana yakice su. Tare da yi musu wulakancin da ko a hanya suka ganshi bazasu yi fatan ace sun san shi ba. Ya fahimci dalibar (obstetric and gynaecology) ce, daga (ID Card) din ta. Yadda ya ga rana haka ya ga dare, ko na second daya bai runtsa ba. So da kaunar student (daliba) Hadiza na narkar mai da zuciya. Abin kamar sihiri, daga ranar bai kara ganin Hadiza ba, bai kuma san ya zai yi ya tambaya ba, tunda ko sunanta bai sani ba. A matsayinsa na babban likita, mai juya sauran likitocin bangaren su, ba karamin zub da kima bane a ji shi yana tambayar wata yarinya cikin masu daukar darasi a wurin su. Duk da haka bai fidda rai ba, yana da yakinin watarana Allah zai sake hada shi da yarinyar ko da a mafarki ne. Ita kuwa Hadiza ba ta dawo TH ba sai bay…