WATA UWA COMPLETE

WATA UWA COMPLETE
WATA UWA COMPLETE ??    WATA UWAR   ??     BY HAERMEEBRAERH Ina mai miqa godiya da Allah da yaban iko nai nufin fara wannan novel mai sunan ??WATA UWAR??, sakamakon wani labari da aka sanar dani dazu da safe, wanda nima shaida ce abubuwa da dama sun faru akan ido na. Naso barin shi a raina amma duba da cewar akwai wadanda ke min magana akan na fara novel, ina ganin ba zan iya ba,? yau nayi tinani nima ina son na bada gudummawa ta ta wannan fanni.? Allah yasa yanda na fara lfy na gama lfy, Allah yasa kuma kuso shi ya amfanar da mu baki daya.❤ Page 1: A guje ta fito daga dakin tana kuka, sakamakon dukan da innar ta ta biyo ta da shi, kamar ba ita ce ta haife ta ba , duka ne ta ke mata da wata qatuwar muciya, wanda in da sabo ta saba, amma da yake na yau yafi na kullum shi ya haddasa mata gigicewa, kuka take tana ” dan Allah inna kiyi hakuri bani bace hinde ce tai fitsarin ta tace nice ya kamata ki gane vani nake yi ba inna” ” sharri kenan kk nufin auta ta zata miki ko?” Inna ba haka nake nu…