WANNAN RAYUWAR CHAPTER 15 KARSHE
WANNAN RAYUWAR CHAPTER 15 KARSHE Da ta farka ta same shi zaune a dakin ta lumshe ido ya mike ya karaso ya kama hannun ta yace “Sannu My love!” Kai ta gyada kawai dan da ta bude ido hawaye ne zai zubo, juyo da fuskar ta yayi yace “Bude idon mana.”+ Bata motsa ba yace “My life!” A hankali ta bude idon ta dake cike da hawaye ai kuwa take ya wanke fuskar ta ya hau zube yace “Ya salam kuka kuma.” Nan ya hau goge mata fuska zatai magana Sadiya ta shigo dakin rike da katon plate da ta dauro fulas fulas na abinci. Ajiyewa taui ta karaso tana fadin “Jikin ne?” Goge hawayen yayi yace “A’ah!” “Ok. Sannu!” “Yauwah.” “Ga abinci fa.” “Ni na koshi.” “A’ah ki kada ci ko kadan ne.” Kai ta girgiza. Sadiya tace “Ko sai anjima.” Kai ta gyada. Ta kalli Kabir tace “Kai fa?” “Nima sai anjima.” “Ok bari naje.” “Ina zaki?” “Daki.” “Me zakiyi?” “Ba komai “ “To xauna kawai.” Kallon Halima tayi ta zauna mikewa zaune tayi Halima sai ta dafe kan ta Kabir yace “Sannu!” Kai ta gyada ta mike ta shiga daki kan gado ta kwanta take kuma wani bacci…