WANNAN RAYUWAR CHAPTER 14
WANNAN RAYUWAR CHAPTER 14 Wani hadadden private hosipital suka je. Suna zuwa yai parking sannan ya fita ya zaga ya bude mata mota. Fitowa tayi ya kama hannun ta. Ta kalle shi tace “Nifa Baby lafiya ta kalou.”+ “K shige muje ko na dauke ke.” Gaba tayi ya mara mata baya. Cikin reception suka shiga suka nufi wajen yankar musu kati sannan aka kai su dakin da zasuga likita. Zama sukai sannan Muhammad ya gaisa da Doctor. Sannan yace “Waye ba lafiya?” Da sauri Fauziyya ta nuna sa shima ya nunata. Dariya Doctor yayi yace “Ikon Allah dukkan kune ba lafiya kenan.” “A’ah ni lafiya ta kalou.” Fauziyya ta fada. Muhammad yai murmushi yace “Kagan ta nan kwana biyu bata jin dadi duk na rasa kan ta. Bata cin abinci amai ma ta gama yanzu da na matsa!” Kallon ta Doctor yai yana murmushi yace “To Madam ya kike ji?” “Nifa ba abinda nake ji. Shine kawai dan ayi min allura.” “Ba zan miki allura ba. Fada min kinji?” “Nifa da safe ne nake zazzabi. Kuma sai naji zuciya ta tana yashi jikina ba kwari.” Rubutu yayi a paper ya da…