WANNAN RAYUWAR CHAPTER 13
WANNAN RAYUWAR CHAPTER 13 Da dare Anty Zainab ta dawo da kayan sannan sukai sallama. Sallah sukai sannan abinci suka ci sannan ta mike ta shiga daki. Wanka tayi ta shirya cikin wasu kayan baccin ta masu kyau. Gajeren wando ne da riga marar hannu sun mata kyau kayan sun kara haska tarure take fesawa ya shigo. Tsayawa kallon ta yayi can kuma ya karasa gaban mudubi ya tsaya ta bayan ta tare da daura kan ta a kafadar ta. Hannun sa kuma ya na kan cikin ta yace ‘Kinyi kyau Zuma ta!” “Nagode!” Dagata yayi ya zura hannun sa a aljihu ya dauko wani box mai kyau budewa yayi taga sarka ce da dan kunne har da zobe na gold. “Ummu kin shayar dani abin da ban taba zato ba kin ban komai a duniya ki bani martabar ki shin ni dame zan saka miki?” “Kai taso na Kawai ya ishe ni.” “Sonki dole ne a waje na Ummu amman ki fadan me kike so bayan shi.” “Ba abinda nake so miji na sai kai kadai.” “Ni naki ne Ummu.” “Godiya nake.” “Ga kyauta Ummu nan bata kai darajar abinda kika ba. amman dan Allah kiyi manage da ita.” Ido ta…