WANNAN RAYUWAR CHAPTER 12

WANNAN RAYUWAR CHAPTER 12
WANNAN RAYUWAR CHAPTER 12 Karfe uku da Rabi an gamai Mata kwalliya amarya tayi kyau cikin peach kala material Wanda akai wa Dinkin doguwar riga sai mayafin kayan da aka dauro Mata a ka aka makele shi. Shigar Tai Mata kyau Kuma Bata nuna tsiraicin ta ba Dan dogon hannu ne Kuma ta bude. Su kansu masu makeup din Basu ta kwalliyar da ta burge su kamar ta Ummu ba. Tayi kyau har ba a magana.+ Sallah tayi tana zaune aka ce anzo daukar ta lokacin hudu da kwata. Mai makeup din da kanta ta rakata har bakin wajen. Wata sabuwar mota ta gani fara tas a wajen tsayawa sukai zata Kira number ya bude motar ya fito. Sanye yake cikin milk din shadda wacce take kyalli ta Masa kyau ya sa bakin takalmi sau ciki ya daura hula Mai kyau da tsada a Kansa. Hannun sa daure da agogon azurfa sai zuba Kamshin yake. Tin da ta daga Kai ta kalle shi Bata Kara dagowa ba Dan yai Mata kyau ba kadan ba. A hankali ya karaso ya kamo hannun ta. Suka wuce wajen mota. Shiga tayi Shima ya shiga sai ya tsaya kallon ta. “Baby Mie King…