WANNAN RAYUWAR CHAPTER 11

WANNAN RAYUWAR CHAPTER 11
WANNAN RAYUWAR CHAPTER 11 Cikin gida suka dawo Hafsa ta shiga daki wayar ta tagani tana haske tana dubawa taga Ahmad ne dauka tayi tai sallama yace “Ina kika shiga ne ina ta kira!”+ “Wallahi na fita naje gun Halima ne!” “Ohk ya jikin nata?” “Da sauki!” “Allah kara sauki!” “Amin” “Daman zan fada miki gani nan karasowa! Zan zo naga my princess naga ita me takara sannan in amshi amsa ta.” Murmushi tayi yace “Toh Allah kawo ka lafiya.” Yace “Amin nagode! Kin shirya kenan” “A’ah!” “In nazo ma kya shirya ai.” “Sai ka karaso.” Ta fada yace “Ok!” Mai fruit ya sama ya siyawa Halima da yawan gaske sanna ya tada mota ya nufi gidan su Hafsa yana mai jin wani farinciki da dadi na ratsa dukkan jikinsa da zuciyar sa. Yana kashe wayar ta mike ta canja kaya sannan ta zauna kirjin ta na dukan uku uku tunanin ta tayaya zata amshi soyayyar sa in taki kuma menene dalilin ta. Tana zaune wayar tabta hau kara dauka tayi ta duba taga Ahmad ne dauka tayi yace “Ina kofar gida!” “Ok!” Ta mike ta saka hijab sannan ta shafa turare ta f…