WA NAKE SO CHAPTER 9

WA NAKE SO CHAPTER 9
WA NAKE SO CHAPTER 9 Alhamdulilah. Sosai na samu kulawa daga gun Momy da likitoci har da nurses da yan uwa na domin kuwa sun yiwa su Momy magana kan kada ana bari na ni kadai dan zan na saka abu a rai na wanda zai kara dagula lafiya ta.+ Wannan yasa ma suka ce a karo mai kula dani dan haka da Momy da Suraiyya muke kwana. Sam basa bari na a kadaici da zanyi wan tunani kuma da safe haka Baba Uwani zata zo da yan gida. bayan sun gamai min allurai sukai sallameni bayan sun kara jawa su Momy kunne akan kulawa dani. Gidan mu Suraiyya ta dawo haka Yaa Kamal ma dan haka sam basa bari na ni kadai. Kullum tare muke yini suyi ta saka ni dariya da labarai. Dan haka sam ban kawo Fu’ad sai naje bacci ko na kwanta nai ta mafarkan sa. Bana kuka a gaban kowa dan da sun ga mood dina ya canja a lokacin duk hankalin su zai tashi suyi ta tambaya ta menene. Kwana na biyar da sallama wanda a lokacin satin Fu’ad biyu da tafiya kenan. Bayan na fito a wanka Momy ta shigo dakin. Mai na dauko ina shafawa tana kallo…