WA NAKE SO CHAPTER 8
WA NAKE SO CHAPTER 8 Sai bayan kwana biyu. Bayan ya shiga gidan gwamnati ya dan yi aiyukan sa. Mikewa yayi ya shirya cikin Bakin glass ya saka da face mask din sa. Nan ya fito kawai ya nemi yan rakiya. Basu san da zasu ba sam sai direction da yake basu. Basuyi mamaki ba lokacin da suka gansu a makaranta domin tin daga shigar Aliyu suka gane zai je ganin wani aikin nasane. Ai kam illai. A bakin gate ya sa aka ajiye sa yace nan da Minti talatin su shigo. Yana shiga ya gaisa da mai gadi. Staff room ya fara zuwa. Ba lafi ba mutane da yawa wannan yasa ya nufi ajijuwa. SS 2b ya fara zuwa ya tadda malami yana ta aikin sa. Har zai shiga SS 3 ya fara ya nufi SS 1 suma aikin ake masa. JS Section ya nufa suma duk ajijuwan da malamai a ciki wannan yasa yayo shashen shugaban makarantar amman sai zuciyar sa tace masa yaje ajikin su Aisha. Kamar ba zashi ba sai ya juya ya nufi SS 2a. Yana zuwa kofar ajin motar da suka zo da ita guda uku suka shigo. Ajin ya shige ya tadda malami. Gaisawa sukai ya fara z…