WA NAKE SO CHAPTER 7
WA NAKE SO CHAPTER 7 Fu’ad da yafi minti goma tsaye akai na ban san ya shigo ba har na fara hawaye sai ji nayi yana gogen hawayen ido na. Wannan yasa na dago a firgice ina kallon sa. Zama yayi a gefe na ya kamo hannu na yace “Dazu muna magana mukai baki right?” Ban amsa masa ba sai wani sabon hawayen dake, zubo min kai ya dafe yana fadin “Fateema ba abinda na tsana na gani kina yi kamar kuka. Ina bawa kai na laifin na na kasa baki farin ciki. Dan Allah ki fada min me yake saki kuka?” Kai ta girgiza masa. Kallon na yake cike da tausawa yace “Ba zaki fadan ba.” Shiru nayi. Janyo ni yayi jikin sa ya rungume ni kamshin turaren sa da nawa suka hadu wannan yasa na lumshe ido. Shima jikin sa sanyi yayi yace “Dan Allah ki daina kukan nan. In kina kuka ina jin kamar ni nai miki laifi.” “Ba kai min komai ba My.” “Kin tabbata?” Kai na gyada yace “Yi baccin ki.” Ya fada yana jijjiga ni a jikin sa kamar jaririya. Bacci ne ya dauke ni dan naji dadin kwanciyyar da nai a jikin sa. In ina tare da Fu’ad ina jin w…