WA NAKE SO CHAPTER 6

WA NAKE SO CHAPTER 6
WA NAKE SO CHAPTER 6 Bashi ya dawo ba sai gab da magariba Dan Yana dawowa ya shiga ya dauro alwala ya tafi masallaci. Acan suka hadu da Abba wanda basu fito ba sai da akai sallah isha’i sannan suka fito a tare sukai bangaren Mai martaba tare da fadawan dake takewa Abbah baya.+ Suna shiga Momy dake da girki na bangaren tana ganin Aliyu ta Bata Rai Sai Kuma ta saki fara’a tana fadin “Barka da zuwa ranka shi Dade!” “Yauwah Fulani. Ya gidan?” “Alhamdulillah!” Waje Aliyu ya samu ya zauna. Sannan ya kalli Abbh yace “Gobe nake son na koma da gudanar da abubuwan da suka Dace.” “To madallah. Allah ya kaimu.” “Amin!” Ya Mike Tare da Dan rusunawa yace “Na barka lafiya. Sai da safe.” “Allah bamu alheri.” Ya juya zai fita sai ga Momy Nan da kuganyu sun shigo rike da tray. “A’ah ina Kuma zaka baka ci abinci ba?” “Alhamdulillah!” Ya fada Yana yin gaba abinsa. ciki suka karasa. Shi Kuma yayi bangaren Mamah Yana shiga suka gaisa sannan ta saka Maryama ta kawo Masa abinci. Zama yayi yaci ya koshi sannan ya kalli Mama…