WA NAKE SO CHAPTER 5
WA NAKE SO CHAPTER 5 Tin daga ranar kullum major AK na dawowa daga gidan gwamnati yake tafiya gidan su Aisha Wanda wani lokacin ma a hanya suke haduwa su karasa tare.+ Sosai suka shaku da juna, Dan kullum zai zo ya koya Mata karatu Wanda In har kana son Aisha ta so ka ko tana kula ka to kana kawo mata zancen makaranta. Wata Ranar alhamis Mamah ta manta Bata bawa yayen Aisha su yo nika ba. Dan har sai da ta daura ruwan tuwon sannan taje Dan ta debo gari tayi talge amma Sai taga Babu wannan yasa ta bawa Aisha taje tayo nika. Amsa tayi tana fita Major AK na karasowa. Murmushi yayi tace “Ina yini?” “Lafiya Lou. Ina zuwa?” Baki ta Dan turo tace “Nika Zan Kai baka ga layi ba Kuma.” Murmushi yayi yace “Shine zakiyi kuka Kuma? Muje na rakaki.” Nan suka fara tafiya suna Hira jifa jifa. Can Aliyu ya kalli Aisha yace “Kanwata ina son ki fada min dalilin ki na son ganin gwamna. Kallon sa ta tsaya Yi sai Kuma ta cigaba da tafiya tana fadin “Baka manta ba Ashe!” “Tayaya zan manta bayan shine dalilin haduwar mu.” …