WA NAKE SO CHAPTER 3
WA NAKE SO CHAPTER 3 A rayuwar ta burin Aisha sam bana ta kyautata tata rayuwar da jin dadi bane sai na ta kyautata rayuwar jama’a ne. Wannan burun nata kuwa tana rasa taya zai kasance duk da a rayuwar ta bata cire rai da kasancewar sa. Sau da dama tana zama tai zurfi a tunanin ta wacce hanya burin ta zai cika. Amman sau da yawa bata samun amsar wannan tambayar. Ita ba inda take zuwa daga makaranta boko sai isilamiyya da Baba ne ke koyar wa ma sai kuwa zaman gida ko gidan su Hauwa. Baba kuwa aikin sa yai nisa dan wajen wata uku kenan suna aiki a gidan Major AK wanda zasu ce basu taba ganin sa ba. Mai gadi ne kawai ke ganin sa shima ta cikin mota ko in ya fito yaga bayan sa. A wata ukun nan Baba ya samu alheri da yawa a aikin da yake inda gida ma suka san da haka dan komai cikin wadata ake musu shi. Major Ak, kuma gwamna a yanzu aiki yake wanda shi dai a kawo masa kwangila yai signing amman bai taba bin aiyukan ya gani yadda suke wakana ba. Haka nan Hajara tayi tsamo tsamo a cikin siyasa dan sa…