WA NAKE SO CHAPTER 2
WA NAKE SO CHAPTER 2 Tin da sukai magana da Shugaban kasa bai kara zuwa ba. Sai katin daurin aure sa mai martabba ya aiko a kawo masa. Shi yasa aka kai office din su da wajen shugaban kasa.+a Duk Aliyu bai san Mai Martabba ya aika ba. Mai martabba yayi aike da sati Aliyu bai da shirin bin sa. Ranar juma’a ne daurin auren amman har labara Aliyu na Abuja. Mai martabba ne ya kira sa. Yana ganin kiran yasan akan mene. Dauka yayi suka gaisa kamar yadda suka saba. “Abbah ya gida?” Ya tambaya duk dan ya kawar da abinda Mai martabba yake son fadi. “Aliyu ince dai ka taho ko?” Mai martaba ya jefo masa tambaya. Kai ya girgiza kafin ya ce, “Abbah sai gobe in Allah ya kai mu.” Dan sanyi Mai martaba yaji dan yasan Aliyu zai iya cewa bai zuwa in kuwa ya fada yasan ta zauna. Aliyu kaifi daya ne, in ya ce, eh ba mai canja masa wannan ra’ayin nasa. “Shikenan. Amman dai da wuri zaka taho ko?” “A’ah Abbah sai wajen dare dan akwai aiki da zanyi.” “Aliyu ya kamata ka dau hutu fa?” “Hutun me Abba?” “Hutun Aure man!” “No Abb…