WA NAKE SO CHAPTER 11
WA NAKE SO CHAPTER 11 Ganin yayi shiru kuma bata daina kallon sa ba yasa ya daura hannun sa a kaffadar ta ya dan girgiza ta a firgice ta dago tana kallon sa cikin tsoro. “Me me… Kace Yaa AK?”+ Ta tambaya muryar ta na rawa daga gani a firgice take sosai. Hannun ta ya kama yana murzawa a hankali. Idon sa ya sa a cikin idon ta. Sannan yace “Aysher! Ki dawo cikin nutsuwar ki, ki saurare ni kiji.” Kai ta girgiza kawai hannun ta rike da nashi yace “Aysher i love u. I really love u Aysher please don’t say no!” Kai ta hau girgizawa tana cire hannun ta daga nashi sannan ta saka a cikin kunnen ta tana karkada su alamar kamar a toshe yake. Sannan ta dago tana kallon sa da manyan idonun ta. Sai yaji ba zai iya jurar kallon idanun nata ba. Kallon sa take babu ko kiftawa. Menene aibun Ya AK babu a yadda ta sanshi babu sam. Mutum ne mai saukin hali da hakuri ba ruwan sa. Yanzu duk yabo da koda wacce yake so ashe ita ce. Zuciyar ta ce ke bugawa da karfi da karfi wanda bata san ko na menene ba. Tasha fada ma…