WA NAKE SO CHAPTER 1
WA NAKE SO CHAPTER 1 A kishingide yake kan wata lallausar dadduma irin ta manyan masu sarauta ta. Ba ajin komai a dakin sai karar AC. Dakin ya gama haduwa da kayan alatu kai ba kace a cikin duniya kake ba. Ga wani haske da ya mamaye dakin mai kara mantar da mutum a Inda yake, Yana sanye cikin shiga ta alfarma. Daga kallo zaka san wannan mutumin ya hada mulki da kudi da mukami. Dan daga yanayin shigar sa da dakin da yake da yanayin walwalar fuskar sa ma abin kallo ne. Sallama aka yi daga bakin kofa. Da kyar ya iya amsawa. Bayan ya dauki fin minti uku da jin sallamar Wani bawa ne ya shigo cikin shigar ja da blue din uniform din su na fada. Zubewa yayi akasa yana fadi, “Allah kara maka lafiya da nisan kwana.” Yana daga kishingide da yake bai ko da motsa ba. Sai Hannu kadai da ya daga masa ba tare da ya kalle shi ba. “Yallabai, Hajiya ce ke son shigowa.” Dagowa yayi a hankali ya aika masa da wani kallo wanda yasa bawan nan shiga cikin hankalin sa. sannan ya kara daure fuska. Ya ce, “Waya fada mat…