UNCLE NE CHAPTER 3 BY NIMCYLUV

UNCLE NE CHAPTER 3 BY NIMCYLUV
UNCLE NE CHAPTER 3  BY NIMCYLUV Jini ya gani ƙwance a saman yatsun hannunsa,cikin takaici da kuma ƙyanƙyami haɗi tashin zuciya ya sanya hannun a jikinta ya goge jinin,ita dai sam bata fahimtar sa banda nishi da riƙe mararta babu abinda take,shuru yyi yana kallon yadda take jijjiga kanta,sam bai san mene zai manta,bai san ta ina zai fara ba,bai san wanne taimako zai mata ba,gaba ɗaya kansa ya kulle,ganin ciwon na neman kasheta ya saka ta miƙe zaune tare da ƙanƙame jikinta ta saka masa kuka,wani mugun haushi take basa amma babu yadda zaiyi dole ya taimaka mata domin shi ɗaya ta sani a gidan, miƙewa yyi tare da saka hannu a bed side ya danne wani abu nan take haske ya gauraye ɗakin,cikin nutsuwa da kamalar data gama ratsa jikinsa ya fara tafiya zuwa parlour kai tsaye wajan fregd ya nufa ya ɗauko bottle water mai sanyi kana ya dawo cikin bedroom ɗin,inda yake ajjiye tablet ɗinsa ya nufa ya ɗauki diflopenic kana ya dawo inda take ƙwace,zama yyi gefe yana tunanin yadda zai mata, Allah ya san…