SIRADIN RAYUWA CHAPTER 8 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

SIRADIN RAYUWA CHAPTER 8 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
SIRADIN RAYUWA CHAPTER 8  BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA       Lokacin daya dawo dare yayi,saidai bawani dare can ba,a sannan sha biyu ne harda rabi,da muqullanshi daya saba amfani yabude gidan yabude yashigo,falon tsit babu kowa kamar yadda yakan tarar kullum idan yadawo,kai tsaye ya haura zuwa sama inda dakinshi yake.        Alwala yasoma yi kamar yadda yasaba zama da alwala akai akai haka ammi takoya mishi tun ba yanzun ba,yakuma saba yatashi da dabi’ar,alqawarin daya yiwa safwa yana cikin ranshi,mutum ne shi mai.matuqar kiyaye alqawari dakuma qoqarin cikashi,don haka yaja laptop dinshi yakunna.        Kiran safwa yasoma yi,wadda tajima gaban system din nata tana tsammanin kiranshi,harta soma kumbura jin shuru har yanzun bai kira ba,saidai idan ta tuna yana da cika alqawari sai kuma fushin nata ya sassauta,don haka yana kira ta daga.        Tarwai ta bayyana cikin screen din nashi,ta cika screen din gaba daya,tana kwance rub da ciki saman gadonta,sanye da wata lafiyayyar baqar riga ta…