SIRADIN RAYUWA CHAPTER 7 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

SIRADIN RAYUWA CHAPTER 7 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
SIRADIN RAYUWA CHAPTER 7  BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA  Baƙiƙƙirin ranta yakekamar yadda fuskarta take a murtuke kai kace saqaon mutuwa aka aiko mata dashi,idanunta na kafe waje daya ranta yana suya,babu wata sauran daraja itakam data rage mata,hotunanta sune abun dauka da turawa wani da namiji?,hawaye taji masu dumi sun taho daidai lokacin dame hoton yagama saisaita komai yafara daukan hotunan.       Ji tayi zuciyarta ba zata iya dauka ba,saboda haka tamiqe ana tsaka da dakn hotunan tawuce zuwa dakin da shine masaukinta,sai data tabbatar data kulle qofa sannan ta sanya kanta jikin qofar tasaki kuka mai ciwo.      Ta jima a haka tana kukanta,wanda ba kowa take kokawa ba wannan karon sai kanta da rayuwarta,sai data gaji don kanta kana taja jikinta zuwa cikin dakin tana fidda kayan jikinta wadanda take jinsu tamkar qaya. **************       Batasan murmushi take ba a sanda take kallon hotunan har rakai qarshensu,lallai lubabatu ta cancanci a qara mata wani abu kan tagomashin da akayi mata…