SIRADIN RAYUWA CHAPTER 6 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

SIRADIN RAYUWA CHAPTER 6 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
SIRADIN RAYUWA CHAPTER 6  BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA Cak qwaqwalwarta ta tsaya da aiki na wucin gadi,komai yayi mata dif tamkar qwaqwalwar tata bata taba wani aiki ba,ta daina fahimtar komai sai maganganun umma luba dake mata amsa kuwwa cikin kunnuwanta,sun dade suna maimaita kansu kafin tasoma fahimtar abinda takeson gaya mata “Taje ta bada fansar kanta da budurcinta wa yariman qasar kaisa na tsahon shekara daya” a dunqule idan ta fahimta kamar hakan umma luba take nufi ko?,ta jefi kanta da tambayar,saita daga idanunta dasuke walainiya ta xubawa umma luba su,shin tasan ma’anar abinda take fada kuwa?,anya hankalinta daya?,a cikin hayyacinta ma take?,bataga alamun wasa saman fuskarta ba face tsantsar gaskiya dason isar da saqo bare tace wasa take mata,karon farko data motsa labbanta  “Ban gane ba umma,ban gane abinda kike nufi ba” murmushi tasakar mata dukka bisa qoqarinta na kwantar mata da hankali “Kin gane maigado saidai kicemin kin rude,kuma tabbas koma wacece da bata zaci samun i…