SIRADIN RAYUWA CHAPTER 5 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

SIRADIN RAYUWA CHAPTER 5 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
SIRADIN RAYUWA CHAPTER 5  BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA Babban club ne na masu aji da naira wanda yake hada manyan yara daga qasashe daban daban matasa masu jini a jiki,daga can wani kebantaccen waje zaka hangeshi zaune saman teburin daya qunshi kujerun zama guda biyar,kowacce kujera akwai mutum akwai,saishi cikon na biyar din dake zaune tsakiyarsu,ba abinda yake bankawa cikinsa hayaqi,wanda duk sanda yazuqa ya fesar sai kaga wani dunqulallen farin hayaqi yatashi sama yacure guri guda kai kace an hura wutar itace ne da jiqaqqen itace ko wutar ta mutune tana neman agajin fifita,daga saman teburin akwai saura saura da burbushin wadanda yasha masu tarin yawa,bayaga kwalbar abunsha wanda babu ko kokwanton cewa ba zallar abunsha bane da baisa buguwa ba.        “Kamal…..ka tsaida wannan hayaqin da kake bugawa cikinka kamar babur,tell us me yake faruwa,kasoma gaya mana kuma but u keep quite”.         Sauran ta hannunsa yayiwa kyakkyawar zuqa sai gata ta qare,yadorata saman table din yakashe k…