SIRADIN RAYUWA CHAPTER 4 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

SIRADIN RAYUWA CHAPTER 4 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
SIRADIN RAYUWA CHAPTER 4  BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA     Ya jima tsaye gaban mudubi yana qarewa kanshi kallo kai kace wata matashiyar budurwa ce data gama ado tanason tantance meye baiyi ba a jikinta tasauya,saidai shi tsaiwar da yayi sam bata da alaqa da irin wannan,yana tsaye ne yana duban kayan da amminsa ta aiko mishi dasu ayau,wanda yana da tabbacin nuni take masa da cewa ya aje qananun kayansa yakoma irin wannan shigar har zuwa lokacin da zaya koma inda yafito.      Kayane irin nasu na sarakai,wanda suka ji aiki ko ina dake nuna zallar sarauta,wani irin yadine ruwan bula mai turuwa wanda aka yiwa aiki da goldin din zare,sai wasu lausassan takalma rufaffu masu wata iriyar lanqwasa daga gabansu,hakanan an shirya musu duwatsu masu haske da qyalqyali daga samansu,takalma ne masu matuqar kyau daraja da tsada na zallar fatar damisa da gashin jimina,sai rawani da aka nada mishi wanda yadace da shigar tasa da kuma kalar kayanshi,yasan kuma ta sanya rawanin ne saboda umarnin data bash…