SIRADIN RAYUWA CHAPTER 3 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

SIRADIN RAYUWA CHAPTER 3 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
SIRADIN RAYUWA CHAPTER 3  BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA Zauna ki lissafa duka ƙannenki ki zabar musu kowa yasaka,yau fulani inajin juyen kayan drower ɗinsu sukayi….ki zaɓa na saida na saidawa,na bada na bayarwa,don ba shakka waɗan nan kaya yadda suke fes kamar ba’a sanyasu ba ƙaramin kuɗi zan samu dasu ba Allah mai gado” murmushi takuma saki wannan karon mai sauti,tana sake jinjina son kuɗi irin na umma luba,kayane masu asalin kyau daraja da tsada,wanda duk wanda ya kalla koda bakasan kuɗinsu ba amma kasani ba masu  ƙarami ko matsakaicin kuɗi bane,tanajin umma luba naci gaba da sambatu gami da bata labarai,ta tsugunna tana duba su hauwa’u tana zaɓarwa kowa,duk da sauran tasan sun musu yawa amma haka ta ɗauka musu,tana kintatar zata bayar a maida musu dai dai jikinsu. “Ana abu a masarautar KAISA,wani abunma sai jibi idan Allah yakaimu” takai ƙarshe tana sakin guɗa,da alamu dai cikin nishadi take yadda ya kamata. Sunan masarautar dataji ya fito daga bakin umma luba sai taji duka kayan sun…