SIRADIN RAYUWA CHAPTER 21 KARSHE BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
SIRADIN RAYUWA CHAPTER 21 KARSHE BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
SIRADIN RAYUWA CHAPTER 21 KARSHE BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA Miqewa yayi daga dosana dawawunshi da yayi saman hannun kujerar daya zauna akai tun dazun yana duba agogonshi,yaga alamar surutun nata bamai qarewa bane,kimanin minti arba’in da zuwanshi kenan amma babu wani abu me muhimmanci data gaya masa,sai soki burutsu da kwashe kwashen zance “Allah ya bamu alkhairi” ya fada yana durfafar qofa,tanason ta sake tsaidashi ta bata mishi lokaci amma kuma ya mata kwarjini da yawa yadda ya hade fuska,hakanan tana kallonshi har ya fice “Ja’iri,wannan baqin ran naka yau za’ayi maganinsa,gwara a soma tarwatsaka,muga qaryar fadin rai da izza,dan banza shi da uwarsa”. Haka kawai ya dinga ji gabanshi na wani irin faduwa,irin faduwar gaban da bai taba jin irinta ba,ya lumshe idanunsa kana ya bude a hankali kuma a fili ya furta “Hasbunallahu wa ni’imal wakil,wala udwana illa alazzalimin” saiya danji faduwar gaban ya ragu,yaci gaba da tafiya a hankali yana dosar sassan nashi,yana kallon yadda sawu…