SIRADIN RAYUWA CHAPTER 20 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
SIRADIN RAYUWA CHAPTER 20 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
SIRADIN RAYUWA CHAPTER 20 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA Tashi rago kawai” kalmar daya fada kenan,firgigit azeez ya bude idanunsa yana ambaton sunan Allah,saiya maida nutsuwarsa jikinsa cikin mamaki ganin me martaba zaune a gabanshi,kanshi ya sadda cikin jin nauyi,sannan a hankali cikin muryar marasa lafiya yace “Barka da asuba” maimakon ya amsa mishi sai yace “Ban taba tsammanin cewa kai din rago bane sai yanzu,shine ka zauna akan mace zaka mutu saboda tsabar ragwantaka?” Shuru azeez din yayi qirjinsa na bugawa,shi kadai yasan me yakeji,yana da tabbacin ba zasu gane ba,yayin da me martaba yaci gaba da kallonshi yana murmushi sannan ya kuma cewa “Dago kanka ka kalleni”yayi maganar yana nade hannun rigar dake jikinsa me zubin alkyabba,dagowar yayi kamar yadda me martaba yace yana dubanshi “ka ganni nan?” Ya fada yana nuna yatsarsa “Ba’a tabani kasani akan mace ba,idan na qudirta a raina saina sameki saina samu…..ka tambayi mamarka….itace babbar shaida,mutum nawa na kasa a mali,na rabota dac…