SIRADIN RAYUWA CHAPTER 2 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
SIRADIN RAYUWA CHAPTER 2 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
SIRADIN RAYUWA CHAPTER 2 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA tunanin idan sukaga rauni a nata idanun yaya nasu zuciyoyin zasu kasance?,saboda haka ta juya kawai tafice a dakin,saidai tana isa tsakar gida ta kasa riqesu suka soma bin kuncinta,tasanya tafin hannunta a hankali tana sharewa gamida dosar gofar fita gida qafafunta kamar ba zasu dauketa ba,duk da bata da yaqinin samun abinda zataje nema,amma tana fatan a dace kodon yaran. Karo suka kusayi da wanda ke ke shigowa,dukkaninsu sukaja baya yana fadi cikin fada fada “Kai,waye wannan?!” “Nice” ta fada a tausashe tana daga kai don ganin waye,sulaiman neyaya a wajenta wanda suka hada uba daya,kusan rabi da rabi yake rayuwarshi a gidan,saboda kaf nauyinsa baikai mahaifinsa,d’a ne ga matar malam bilya ta farko wadda suka jima da rabuwa,tafiye tafiye yake qwadagonshi da neman kudinsa,kuma ba laifi yana samun na rufawa kanshi asiri,duk da bai tsinanawa uban komai sai abinda yaga dama,saboda haushi da takaicin yadda ya watsar da rayuwarsu dake…