SIRADIN RAYUWA CHAPTER 18 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
SIRADIN RAYUWA CHAPTER 18 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
SIRADIN RAYUWA CHAPTER 18 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA Kyakkyawar budurwa ce zaune gefan gadon kara sanye da kayan saqi,kyakkyawar fuskar hauwa’unta data sha yabawa tana qissima girmanta,ba shakka hauwa’u ce,saboda babu wani sauyi da zai saka ta kasa gane fuskar daya daga cikin ‘yan uwanta,musamman hauwa’un da kullum take kwana ta kuma tashi da begen son ganinta. Batasan ta kirayi sunanta ba sai da taga mutanen dake cikin bukkar dukka sun waiwayo suna kallonta,har ita hauwa’un da kanta ke kallon qasa a dazun,miqewa taga tayi daga bakin gadon karan tana fiddo idanu “Yaaya maigado!” Ta fada da sauri kana cikin wani mugun gudu tayo inda take,ba bata lokaci ta fada jikin bilkisun suka rungume juna,lokaci daya kuma suka fashe da kuka,wanda ya janyo hankalin na kusa dana nesa,suka tattaru a wajen suka tsaya carko carko suna kallon sarautar ubangiji. Daidai lokacin da anty zuhriyya da kanta ke ratso wajen saboda dadewar da taga bilkisun ta danyi,gashi suna son wucewa,sai tsoro ku…