SIRADIN RAYUWA CHAPTER 16 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
SIRADIN RAYUWA CHAPTER 16 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
SIRADIN RAYUWA CHAPTER 16 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA Kusan awa guda kenan yana tsaye qofar shiga da fita na hotel din yana jiran ganinta,wayarshi na hannunsa,lokaci lokaci yakan maida kanshi ya danna na wasu sakanni sannan ya sake daga kanshi idan yaji qarar fita ko shigar wani abun hawan. A irin hakanne motar da suke ciki ta durfafi gate din,yayi jinkirin daga kanshi wannan karon sai da suka kusa giftashi,a sannan idanunsa suka sauka kanta daga,tana zaune daga gefan hannun hagus saitin da yake,kafin yayi wani yunquri tuni sun harba titi,hakan ya sanya baiyi qasa a gwiwa ba shima ya tsaida taxi ya rufa musu baya don yana son cimmata a duk inda zata je. A qalla azeez ya kusa shafe rabin sa’a a bakin dakin taron,duk bayan wasu mintuna saiya duba agogon hannunsa yana jiran lokacin zuwan nasu ya cika,dubawa ta qarshe agogon ya nuna masa nan da mintina biyar zasu iya isowa,hakan ya sakashi fitowa daga cikin hadaddiyar motar tasa,ya haye samanta ya zauna,ta saitin daya tabba…