SIRADIN RAYUWA CHAPTER 15 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
SIRADIN RAYUWA CHAPTER 15 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
SIRADIN RAYUWA CHAPTER 15 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA Mintina qalilan afnan ta dawo ta kammala,ta miqa masa plate din dake a rufe,da idanu ya mata alama takai mishi daki,saita juya zuwa dakin,cikin ranta tana mita da qunqunin rashin ganin amfanin matarsa,da ba zata iya tsaya masa kan cikinsa ba,da sun hada muhalli saidai su suyita hidima dashi,komai tafison a mata tana daga zaune yadda take tun daga gidansu. “Munyi waya da mai martaba,yace ya kamata mu dawo gida hakanan,saboda jama’ar dakeson yi muku gaisuwa” kai ya jinjina sannan yace “Kamar yaushe ya kamata kenan mu tafi,tunda ticket kawai zamu siya” dan shuru tayi kadan sa’an nan ta dora “Idan ba damuwa nan da jibi ya kamata mu wuce” ya sake jinjina kanshi “Shikenan,babu damuwa,gobe zanje na karbo certificate din mutuwar suhaima,jibin saimu wuce in sha Alla” ajiyar zuciya fulani ta sauke mai nauyi sannan tace “Allah yayi mata rahama” “Ameen ameen ya Allah” ya fada yana sadda kanshi qasa,shuru ya ratsa falon na wasu mint…