SIRADIN RAYUWA CHAPTER 11 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

SIRADIN RAYUWA CHAPTER 11 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
SIRADIN RAYUWA CHAPTER 11 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA Sannu a hankali ta soma qoqarin bude idanuwanta da sukayi mata wani irin nauyi,a qalla ta dauki kusan minti daya tana wannan fafutukar sannan tasamu ta budesu tana warasu dakyau don su daina ganin dishi dishi,cikin ikon Allah ganinta ya daidaita,saita sake ware idanun nata tana kallon dakin da take ciki.       Da fari bai mata kama da dakin asibiti ba,sai data lura da wasu abubuwa da suke kamanceceniya dana asibiti sannan ta tabbatar tana cikin dakin asibiti ne.     Babu kowa cikin dakin,sai fanka da ac da suke aikinsu cikin madaidaitan sanyin da bazai takura ka koya hanaka sukuni ba.        Kallonta tayi qoqarin maidawa bakin qofa sanda taji an turo qofar,anty zuhriyya ce karo na biyu,qara saurinta tayi don ta iso gareta,fuskarta washe da fara’a sosai tana duban bilkisu,bata tsaya ko ina ba sai kujerar dake gaban gadon,wanda dama ita ta tashi daga kai,ta sanya hannunta ta kamo hannun bilkisu guda daya,murmushi da hawaye na qwace m…