SIRADIN RAYUWA CHAPTER 1 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

SIRADIN RAYUWA CHAPTER 1 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
SIRADIN RAYUWA CHAPTER 1 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA _akwai yiwuwar ganin sabbin qirqirarrun sunayen garuruwa da gurare_  1995  *Tushen Labarin*  Malam bilyaminu usman,haufaffen bafulatanin nijer a haihuwa da yare,ta wani fannin kuma d’an qasar *KAISA* kuma bahaushe magidanci mai halayya da dabi’u da al’adu irin na wasu daga bara gurbin hausawa,wadanda basu gama fahimtar abinda addini yayi magana akai ba kan iyali da haqqoqinsu dake bisa wuyan dukkan wani magidanci,walau saboda jahilci ko kuma sun take ne da  gangan bisa son zuciyarsu da soye soyen rayuka.  Haifaffen agadez iyayensa dukkaninsu suka kasance xallar fulanin niger,fatauci da neman kudi yakawoshi gasar kaisa,wanda a yanzun ita tazame masa mazauni  na dindin.  Shiga da saninki kusan shine laqabin da mutane suka yiwa gidansa bayan da halayyarsa tafito garara na auri saki,mutum ne ma‘abocin aure aure,wanda har hakan yazame masa jini da tsoka,bai kuma daukeshi a wani abun aibu ko abun Allah wadarai baya auri mata aqalla da suka d…