RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 3 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 3 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA  BOOK 1  CHAPTER 3  BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO Www.bankinhausanovels.com.ng  A JIYA MUN TSAYA  Yau Asabar bayan ya tafi wurin motsa jika ya wuce Islamiyya daga nan, da _ yake Islamiyyarsu ba daya ba ne da Kannansa, don haka ya dawo gida ya zauna daga farfajiyar gidan ya kurawa Kasa idanu yana kallo. Ya rasa tunanin me yake yi, kunnuwansa suka jiyo masa kukan jariran. Tashi ya yi ya nufi dakin renonsu, a nan ya sami Haidar da Hafsat da bulalai suna tsulawa jariran nan. Babu kowa akansu, hakan ya tashi hankalin Sultan ya jawo su, ya yi masu  wani irin mugun duka, wanda ya dasa masu  ZAMU TASHI   soron shi fiye da tunanin su, kasancewar bai taba kai hannu jikinsu ba. . Hajiya Salma ta fito a gujen gaske tana ganin abinda ya faru, ta sa Salati da Karfi tare da dafe Kirji. Tana Karasowa ta dauke shi da mari. Ya rike fuskarsa zuciya tana wani irin cinsa. Ji yake kamar dukan da ya yi masu bai gamsar da shi ba, yana jin zai iya aikata komai akan yaran da ya Kwallafa ransa a kansu.…