RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 1 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 1 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 1 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO Wannan ma littafi ne da zamu dinga kawo muku shi a wannan website namu kudai ku kasance damu a koda yaushe Www.bankinhausanovels.com.ng KADUNA Da yammacin ranar Alhamis ne, Allah ya yalwata garin na Kaduna da ruwan sama. Hakan ya jawo boyewar jama’a da dama domin fakewa ruwan. Ruwane ake tsugawa mai Karfi kamar zai fasa saman kwanukan jama’a. Cikin hukuncin na Rabbi, wanda ya saukar da ruwan ba tare da wayonmu ko dabararmu ba, ya tsaida abin shi cak! Cikin lokaci Kalilan. Hakan ya sa jama’ar da ke Boye suka fara firfitowa kowa na KoKarin kama gabansa, domin gab ake da kiran Isha’i. A irin wannan yanayin da za ka ci nasarar leKa dakunan jama’a za ka tsinci kowannen su a Kundudune cikin rigar sanyi, ko kuma bargo. Marasa Karfi kuwa, irin almajirai da sauran su, suna Kudundune a lungu ko kuma cikin zannuwa. Alhaji Lukman ne zaune a mazaunin direba, yana tafiya a natse bisa shimfidaddiyar kwalta, fuskarsa babu alamun gajiya ko …