RAUDHA CHAPTER 9
RAUDHA CHAPTER 9 Biri da wando ta saka me santsi Light orange, ƙasan wandon me fela ne sosai, sai ta saka top fari iya gwiwar ta, me kwalliyan stones, sannan sai ta naɗa blue ɗin ɗankwali a kanta, wanda ya fito mata da gashin ta ta ƙasan ƙeya, Light makeup tayi da ya fito da tsantsan kyawun ta, kai Masha Allah duk wanda ya ga RAUDHA wannan lokacin bazai so ya ɗauke idanun sa ba, ta haɗu iya haɗuwa sai wanda ya gani, takalmin da ta saka me tsinin gaske ne cover me igiya, kalan Light blue da farin Socks a ciki, sai tashin ƙamshi take yi irin turaren nan na Arabian+ Ramcy dake zaune saman sofan ɗakin ta, sakin baki tayi tana kallon ta Sai da RAUDHA ta matso kusa da ita, ta sanya hannun ta ta shafa fuskar ta tana murmusawa. Sannan a time ɗin Ramcy ta rufe bakin ta bayan ta dawo da tunanin ta jikin ta “What happened Besty?” Gwauron numfashi Ramcy ta sauke kafin tace, “ban san me zan ce bane wlh Besty, haɗuwar ki yayi yawa. Masha Allah gaskiya ki gode Allah”. Murmushin ta me kyau ta saki kafin t…