RAUDHA CHAPTER 8
RAUDHA CHAPTER 8 don Allah yasa Daddy me saurin yarda da ƙaddara bane, da babu abinda zai sa be zube musu anan ba, sai dai kuma sosai ya dage wajen danne kaso sittin cikin ɗari na daga damuwar sa, amma hakan be sa fuskar sa ta hana bayyanuwar tsantsan damuwa da tashin hankalin da yake ciki ba, idanuwan sa gaba ɗaya sun kaɗa sun yi jazur, muryan sa na rawa ya ce da su, “yanzu tana asibitin ne?”+ Rayyan ya ba shi amsa da “Eh”. “Ok ku mu je ku kai Ni”. Yafaɗa yana miƙe wa tsaye da hanzari Tare suka fice suka shiga motar Suhaib, Rayyan ne ya ja su zuwa asibitin. Suna isa ɗakin da aka kwantar da RAUDHA, Daddy yayi saurin ƙarisawa wajen ta, zama yayi ya ɗaura tafukan hannayen sa biyu saman fuskar ta yana shafa wa, ji yake yi tamkar yayi ta kurma kuka sabida tsananin tausayin ɗiyar sa. Wai yau RAUDHA ce kwance cikin wani hali na taɓin hankali, duk a sabida sakacin su Lumshe idanu yayi yana sake sauke wa akan kyakkyawar fuskar ta, wanda ya rame sosai, sai haske da ta sake yi, barci take yi ha…