RAUDHA CHAPTER 6

RAUDHA CHAPTER 6
RAUDHA CHAPTER 6 Baby kin ga me sunan Daddy? Yana kama dake ko?” + RAUDHA da ta ƙura wa jaririn idanu ko ƙifta wa ba ta yi, ko taɓa sa ta kasa yi illa gyaɗa wa Yayan nata kai da tayi Murmushi yayi don ya san halin ta akwai tsoron ƙananan yara, don ya tsokane ta yace, “ki ɗauke sa mana kar yayi fushi dake”. Maƙe kafaɗa tayi “Baby Daddy ne fa, ko ba kya son sa?” Har yanzu idanun nata akan jaririn yake taƙi dena kallon sa, cikin muryan ta da baya fita ko kaɗan tace, “yaya ka bari sai ya sake girma zan na riƙa ɗaukan sa”. Dariya kawai Suhaib yayi, yana sake rungume yaron nasa tare da sumbatar sa.      Lokacin ne Inna Haule tashigo ɗakin tana faɗin “a’ahh Mijina ashe kana nan ne?” “Eh Inna, na rako RAUDHA ganin Baby ne”. “To madalla, ai ga ta nan kuwa ta kafa masa idanu amma taƙi ta ɗauke sa”. cewar Inna cike da fara’an ta Suhaib dariya yayi yana kallon RAUDHAN, kafin yace, “Baby baki gaishe da Inna ba”. Sai alokacin ma RAUDHA ta kalle ta tun shigowar ta, gaishe ta tayi kamar yanda Suhaib yace mata Inn…