RAUDHA CHAPTER 4

RAUDHA CHAPTER 4
RAUDHA CHAPTER 4 Iska yafesar ta cikin bakin sa kafin yace “Nasan tana sha ai”. + Baki sake Farida take kallon sa, cike da tsantsan mamakin sa tace “kana nufin kana sane tana wannan rayuwan but bakayi komi akai ba?” Zuwa yanzu damuwa ne sosai yanuna a face ɗin nasa, cikin rashin jin daɗin halin da ƙanwar nasa take ciki yace “Ni kaina bana jindaɗin halin da Baby take ciki amma bansan ya zan yi ba, na rarrashe ta na faɗa mata illan hakan but taƙi ji”. Ido Farida tazuba masa ta kasa cewa komi, mamaki al’ajabi duk ya cika mata zuciya, bata taɓa tunanin soyayyan da suke mata zai saka su bar ta tana irin wannan rayuwan ba, a matsayin ta na ɗiya mace ma ba na miji ba “Lallai kam akwai aiki”. Tafaɗa a ranta kafin a fili tace “Wannan wani irin so kake mata da har zaka kai ta ga halaka?” Tsare ta da idanu yayi cikin rashin fahimta yace “me kike nufi Wifey?” “Ina nufin taya zaka bar RAUDHA tana shaye-shaye but ka kasa hana ta? Kana tunanin halin da zata shiga nan gaba? Meyasa soyayyar ta zai rinjaye ka …