RAUDHA CHAPTER 11 KARSHE

RAUDHA CHAPTER 11 KARSHE
RAUDHA CHAPTER 11 KARSHE ? Murmushi ne ya suɓuce a kan kyakykyawar farar fuskar sa, sai dai be iya cewa komi ba illa kallon ta da yake yi+ While itama ta kasa ɗauke idanun ta kansa, sai dai a wannan lokacin sosai fuskarta ta kumbura da ɓacin rai, cike da fushin da bata san na mene ne ba tace, “ba’a gaya maka nan ɗin inda zan ajiye baƙo na bane da zaka zo ka zauna?” Sai kuma ta juya tana kwaɗa wa Saude kira, taku ɗaya biyu tayi ta tsinkayi muryan sa yana faɗin “Pretty ki bar wahalar da kanki mana, Ni ne Ƙalby ɗin ki”. Cakk ta tsaya tana juyo wa gare sa, ido cikin ido take kallon sa but ta kasa magana, sai kai komo da zuciyar ta ke yi wajen bugawa da ƙarfi Murmushi ya sake yi yace, “nasan zaki yi mamaki da jin kalamai na, but ba abun mamaki bane, na shirya tsab don bayyana miki Ni ne wanda kike soyayya dashi batare da kin san ko waye ba, Pretty Ni ne Ƙalby ɗin ki, wanda kike matuƙar ƙauna da..” Tsayar dashi tayi ta hanyar ɗaga masa hannu da faɗin, “ya ishe ka da Allah Malam”. Sake ware idanun …