RAUDHA CHAPTER 10

RAUDHA CHAPTER 10
RAUDHA CHAPTER 10 _______? Sun Isa Bayelsa wajen gabanin magriba, driver ya zo ya kwashe su ya nufi da su tanƙamemen gidan su, gidan flet ne me kyan gaske+ Suna shiga parlour’n matasan duk suka wuce ɗakunan su, inda Ammee ta nuna wa RAUDHA ɗakin da zata zauna, tana fita ta shiga Toilet tayi wanka sannan ta ɗauro alwala, doguwar riga blue ta saka kafin ta gabatar da sallah Bayan ta idar ta fito Parlour, babu kowa sai Ammee da itama zaman ta kenan Tace, “ƙariko mana ɗiya ta”. Taho wa tayi ta zauna a gefen ta Ammee na murmushi tace, “kin ji sabon wuri, da fatan dai ya miki?” Itama murmushin tayi tace, “Yayi min Ammee”. “To Masha Allah haka nake so, bari in saka a kawo miki abinci ko kina jin yunwa”. “A’a Ammee a bari sai anjima zan ci”. Ammee tace, “to shikenan, kinga dai gidan mu ko. Nasan yanzu dare yayi ne shiyasa babu wanda zai zo sai zuwa gobe zaki ga ƴan uwa, Family House ɗin mu na nan baya ne, mutanen gidan duk ƙannin Uncle ne da matan su da ƴaƴan su, zuwa gobe insha Allahu sai mu je ku gai…