RAUDHA CHAPTER 1
RAUDHA CHAPTER 1 __________? Alarm ɗin da tasaita ƙarfe 09:00pm. Yatashe ta daga barcin da take yi, a hankali tayaye bargon da tarufe jikin ta har kanta dashi tasoma miƙa tana hamma, ɗakin gaba ɗaya duhu ne don ba’a ganin komi, miƙewa zaune tayi ta jima ahaka har magagin barcin da take yi yasake ta kafin tazuro ƙafafun ta tasauko daga gadon tanufi wajen makunnin ɗakin takunna wuta, haske ne yamamaye gaba ɗaya ɗakin da yatsaru iya tsaruwa, komi na ɗakin Sky Green ne, takowa tayi ta’isa gaban gadon tana sake zama, hannu tasanya tadafe goshin ta na tsawon mintuna 3 kafin tasoma tattare gashin kanta da yake abaje har zuwa kafaɗun ta taɗaure da jelan gashin, miƙewa tayi tasoma cire kayan barcin jikin ta sannan taɗaura towel tashige toilet, tana shiga tasakarwa kanta shower, sai da tadaɗe tana jiƙa ƙanta daga sama har ƙasa kafin tasoma wankan, acikin mintuna 15 tagama taɗauro showel tafito, a gaban dressing mirror tazauna tasoma tsane kanta, sai kuma taɗau handrayer tafara busar da gashin t…