NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CHAPTER 3 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CHAPTER 3 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI
NA SHIGA ALJANNAH  BOOK 1  CHAPTER 3  BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI Www.bankinhausanovels.com.ng  A JIYA MUN TSAYA  To babu laifi, Allah ya zaba mafi alkhari. Idan an samo sana’ar sai a sanar damu mu taya Murna. Tashi kaje”  ZAMU TASHI ****** Garin Kano garin kasuwanci, unguwar kurawa unguwar sarakai. kuma unguwar maķotaka da kasuwar rimi bakin asibiti. – An ce duk mai makotaka da kasuwa baya tsiya, amma da alama wannan Kaulin ya tsame Adamu ciki, domin a Kurawa aka haife shi, ya girma a cikinta amma yau ya laluba sana’ar yi ya kasa ganowa ko kuma ita ta kasa ganinsa, – saboda haka kamar makotaka da kasuwar ta kasa yi masa rana. ° Bayan alhinin awa daya kacal~ wanda yayi bayan turin je-ka-ka-mutun da Alh. Yayi masa, ya dawo gida ya dinga cakuda rayuwa da mutuwa a hakuri da son Husna da kuma sauran rayuwarsa, da kyar ya wafto jarumtar tashi ya “nemo sana’a don kar ya mutu a matsayin ragon soyayya da rayuwa, tunda aikin malam ba lallai nan take zai ci ba. Www.bankinhausanovels.com.ng Amma kaico! K…